Ezra 6:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima. Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ اللَّهْ وَنْدَ يَسَا سُونَنْسَ يَكَسَنْثٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ، يَتُمْٻُكٜىٰ كُواْوَنٜىٰ سَرْكِے كُواْ مُتَنٜىٰ وَطَنْدَ ذَاسُيِ ڧُواْڧَرِ سُثَنْجَ وَنَّنْ دُواْكَا كُواْ كُوَ سُهَلَّكَرْ دَ غِدَنْ اللَّهْ أَ عُرُوشَلِيمَ؞ نِے سَرْكِے دَرِيُسْ نَكَڢَ وَنَّنْ دُواْكَا، بَرِ عَكِيَايٜىٰ دُواْكَرْ دَ ثِكَكِّيَرْ أَنِيَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”