Ezra 6:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ دَتَّاوَنْ يَهُودَاوَا سُكَ ثِيغَبَدَ غِنِنْ سُنَ كُمَ سَامُنْ يَلْوَتَ تَوُرِنْ ڧَرْڢَڢَاوَرْ أَنَّبْثِنْ أَنَّبِے هَغَّيْ دَ أَنَّبِے زَكَرِيَّا طَنْ إِدُّواْ؞ سُكَ غَمَ غِنِنْ بِسَغَ يَدَّ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَعُمَرْثِ سَيِرُسْ دَ دَرِيُسْ دَ كُمَ أَرْتَظٜىٰكْظٜىٰسْ، سَرَاكُنَنْ ڢَٰشِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.