Ezra 6:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَبِكٍ كٜىٰٻٜىٰ غِدَنْ اللَّهْ مُتَنٜىٰنْ سُكَ مِيڧَ هَدَايُنْ بِجِمَيْ طَرِے دَ رَغُنَ طَرِے بِيُ دَ یَنْ تُمَكِ طَرِے حُطُ؞ سُكَ كُمَ مِيڧَ بُنْسُرَيْ غُواْمَشَا بِيُ دُواْمِنْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ دُوانْ كُواْوَثٜىٰ ذُرِيَ تَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu,da 'yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra'ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra'ila.