Ezra 6:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin ’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا دُكَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا سُنْ رِغَا سُنْ ڟَبْتَثٜىٰ كَنْسُ، دُكَنْسُ كُوَ سُكَ ذَمَ مَرَسَ ڧَظَنْتَا؞ سَيْ لَوِيَاوَا سُكَ يَنْكَ طَنْ ضَغُواْ نَبِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ دُواْمِنْ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ كُواْمُواْ دَغَ بَوْتَا، دُواْمِنْ یَنْعُوَنْسُ ڢِرِسْتُواْثِے دَ كُمَ دُواْمِنْ سُو كَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama firistoci da Lawiyawa sun tsarkake kansu, suka kuwa tsarkaka, sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewa saboda dukan waɗanda suka komo daga bauta, da kuma saboda 'yan'uwansu firistoci, da su kansu.