Ezra 6:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ سُكَ كُواْمُواْ دَغَ بَوْتَا، تَرٜىٰدَ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ وَارٜىٰ كَنْسُ دَغَ رَايُوَرْ ڧَظَنْتَا تَڧَبِيلُنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ عَڧَسَرْ دُواْمِنْ سُبِے يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، سُكَثِ طَنْ ضَغُواْ نَبِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Isra'ila waɗanda suka komo daga zaman talala suka ci tare da kowane mutumin da ya haɗa kai da su, ya kuma keɓe kansa daga ƙazantar al'umman ƙasar, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila.