Ezra 6:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce, Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَثِكِنْ شٜىٰكَرَا تَڢَرْكُواْ تَمُلْكٍ سَرْكِے سَيِرُسْ، يَبَادَ عُمَرْنِ غَمٜىٰدَ غِدَنْ اللَّهْ أَ عُرُوشَلِيمَ؞ يَبَادَ عُمَرْنِ أَ سَاكٜىٰ غِنَا غِدَنْ، وَتُواْ وُرِنْ دَ ذَاعَ مِيڧَ هَدَايُ؞ بَرِ عَكَڢَ تُوشٜىٰنْ غِدَنْ، عَكُمَسَا ڟَيِنْ غِدَنْ يَكَيْ ڧَڢَا ثَسَعِنْ، ڢَاطِنْ كُمَ يَكَيْ ڧَڢَا ثَسَعِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A shekara ta fari ta sarautar sarki Sairus, sai ya ba da izini a sāke gina Haikalin Allah da yake a Urushalima, wurin da za a miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Sai a aza harsashi da ƙarfi. Tsayinsa zai zama kamu sittin, fāɗinsa kuwa kamu sittin.