Ezra 6:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَنْدَ حَكَ إِنَبَادَ عُمَرْنِ غَمٜىٰدَ أَبِنْدَ دُواْلٜىٰ ذَاكُيِ دُواْمِنْ كُتَيْمَكِ وَطَنَّنْ دَتَّاوَنْ يَهُودَاوَا دُواْمِنْ سُسَاكٜىٰ غِنَا وَنَّنْ غِدَنْ اللَّهْ ؞ «عَبِيَ كُطِنْ عَيْكِ غَ مُتَنٜىٰنَّنْ دَغَ مَعَجِنْ غِدَنْ سَرْكِے، وَتُواْ كُطِنْ هَرَاجِ دَغَ يَنْكِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ؞ عَبِيَسُ ثِكَكّٜىٰنْ كُطِنْسُ بَابُ ٻَاتَ لُواْكَثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ina umartarku ku biya wa dattawan Yahuza kuɗin sāke ginin Haikalin nan na Allah, a biya mutanen nan cikakken kuɗin aiki daga baitulmalin sarki, wanda yake a lardin Yammacin Kogi, ba tare da ɓata lokaci ba.