Ezra 6:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su ’yan bijimai, da raguna, da ’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُبَا ڢِرِسْتُواْثِنْ دَسُكٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ دُكْ أَبِنْدَ سُكٜىٰ بُڧَاتَ كُواْوَثٜىٰ رَانَ بَابُ ڢَاسَوَ؞ كُبَاسُ یَنْ بِجِمَيْ، كُواْ رَغُنَ، كُواْ یَنْ تُمَكِ دُوانْ يِنْ هَدَايُنْ ڧُواْنَاوَا غَ اللَّهْ نَ سَمَ؞ كُبَاسُ أَلْكَمَ، كُواْ غِشِرِ، كُواْ ضُوً إِنَبِے، كُواْ مَنْ ظَيْتُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ba su duk abin da suke bukata, wato kamar 'yan bijimai, da raguna, da 'yan tumaki domin yi wa Allah na Sama hadayun ƙonawa, da alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da man naɗawa yadda firistoci a Urushalima suke bukata, sai a ba su kowace rana banda fashi,