Ezra 7:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu ina ba da umarni cewa duk wani mutumin Isra’ilan da yake cikin mulkina, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da suke so su tafi tare da kai zuwa Urushalima za su iya tafiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«إِنَ بَادَ عُمَرْنِ ثٜىٰوَ كُواْوَنٜىٰ مُتُمِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُواْ ڢِرِسْتُواْثِنْتَ كُواْ لَوِيَاوَنْتَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَيَنْكِنْ مُلْكِنَ، دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰدَ نِيَّ يَكُواْمَ عُرُوشَلِيمَ تَرٜىٰدَكَيْ، سَيْ يَتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra'ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.