Ezra 8:16 โ Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waษanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waษanda masana ne.
Hausa Arabic 2020 (ุงููุชููููุฑูุชู ุฏู ุงูููููุจูุงููุง)
ุณูููููุณูุง ุนูููุฑูุง ู
ููู ุนูููฐููููููฐุธูููฐุฑู ุฏู ุงููุฑูููููฐูู ุฏู ุดูููฐู
ููู ุฏู ุนูููฐููููุชููู ุฏู ููุฑูุจู ุฏู ุนูููฐููููุชููู ุฏู ููุชููู ุฏู ุฒูููุฑููููุง ุฏู ู
ูููฐุดููููู
ูุ ุดููุบูุจูููู ููููฐููููุ ููููู
ูุณูุง ุนูููุฑูุง ูููุงูููุฑูุจู ุฏู ุนูููฐููููุชูููุ ุบูู
ูุง ุณูู ู
ูุงุณู ุญูููู
ู ููููฐุ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na sa a kirawo Eliyezer, da Ariyel, da Shemaiya, da Elnatan, da Yarib, da Elnatan, da Natan, da Zakariya, da Mehullam waษanda suke shugabanni, a kuma kirawo Yoyarib da Elnatan masu hikima.