Ezra 8:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَكُمَ عَيْكٜىٰسُ ذُوَا وُرِنْ إِدُّواْ شُوغَبَا أَ كَسِڢِيَ؞ نَڢَطَا مُسُ أَبِنْدَ ذَاسُ ڢَطَا وَ إِدُّواْ دَ سَوْرَنْ یَنْعُوَنْسَ مَاسُ يِنْ حِدِمَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ أَ كَسِڢِيَ، دُواْمِنْ سُأَيْكُواْ مَنَ مَاسُ يِنْ حِدِمَ أَ غِدَنْ اللَّهْ نْمُ أَ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na kuma aike su zuwa wurin Iddo, shugaba a Kasifiya. Na faɗa musu abin da za su faɗa wa Iddo a Kasifiya da 'yan'uwansa ma'aikatan Haikali, wato ya aiko mana waɗanda za su yi hidima a Haikalin Allahnmu.