Ezra 8:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ كُواْمُواْ دَغَ ڧَسَرْ بَوْتَا سُكَ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا غَ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ سُكَ مِيڧَ بِجِمَيْ غُواْمَشَا بِيُ دُواْمِنْ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ رَغُنَ ثَسَعِنْ دَ شِدَ دَ یَنْ تُمَكِ سَبَعِنْ دَ بَݣَويْ؞ سُكَ كُمَ مِيڧَ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ دَ بُنْسُرَيْ غُواْمَشَا بِيُ؞ عَكَ مِيڧَ دُكَنْ وَطَنَّنْ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra'ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra'ila,da raguna tasa'in da shida, da 'yan raguna saba'in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.