Ezra 9:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ كَدَ مُسَا یَیَنْمُ مَتَ سُعَوْرِ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ كُواْ یَیَنْمُ مَظَا سُعَوْرِ یَنْ مَاتَنْسُ؞ كُمَ كَدَ مُتَٻَ تَيْمَكُوانْسُ كُواْ مُنٜىٰمِ ذَمَنْ لَاڢِيَرْسُ؞ تَهَكَ ذَامُيِ ڧَرْڢِے مُجِ دَاطِنْ ڧَسَرْ، مُكُمَ بَرْ وَ یَیَنْمُ ڧَسَرْ تَذَمَ أَبِنْ غَادُوانْسُ حَرْ أَبَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka kada ku aurar musu da 'ya'yanku mata, kada kuma ku auro wa 'ya'yanku 'yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga 'ya'yanku har abada.’