Ezra 9:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da na ji wannan, sai na yaga rigata da alkyabbata, na tsittsige gashin kaina da na gemuna, na zauna, na rasa abin da yake mini daɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ نَجِ وَنَّنْ سَيْ نَيَيَّاغٜىٰ رِيغُنَنَ، نَثِثِّرٜىٰ غَاشِنْ كَيْنَ دَ نَغٜىٰمُنَ، سَيْ نَذَوْنَ، نَرَسَ أَبِنْ ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.