Ezra 9:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai duk waɗanda suke tsoron maganar Allah na Isra’ila suka kewaye ni don su ji wannan rashin imani wanda waɗanda suka dawo bauta suka yi. Na kuwa zauna a can a rikice, har lokacin miƙa hadaya na yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً دُكَنْ وَطَنْدَ مَغَنَرْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ تَسَا سُيِ ضَوَرْ جِكِے سَبُواْدَ رَشِنْ أَمِنْثِنْ مَاسُ كُواْمُواْوَ دَغَ ڧَسَرْ بَوْتَا، سُكَ تَارُ كٜىٰوَيٜىٰ دَنِے؞ نَاكُوَ ذَوْنَ، نَرَسَ أَبِنْ ڢَطَا حَرْ لُواْكَثِنْ هَدَايَ تَيَمَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan dukan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra'ila, saboda rashin aminci na waɗanda suka komo daga zaman talala, suka taru, suka kewaye ni sa'ad da nake zaune a ruɗe, har lokacin yin sadakar yamma.