Ezra 9:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tun daga zamanin kakanninmu har zuwa yanzu, zunubanmu suna da yawa. Domin zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu aka kama mu, aka wulaƙanta mu, muka zama bayi a hannun sarakuna waɗansu ƙasashe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْدَغَ زَامَانِنْ كَاكَنِّنْمُ ذُوَا يَوْ، مُنْيِ بَبَّنْ لَيْڢِے؞ سَبُواْدَ ذُنُبَنْمُ، مُو دَ سَرَاكُنَنْمُ دَ ڢِرِسْتُواْثِنْمُ، مُكَ ڢَاطَ أَ حَنُّنْ سَرَاكُنَنْ أَلْعُمَّيْ؞ عَكَ كَكَّشٜىٰمُ، عَكَ ݣُوشٜىٰمُ ذُوَا ڧَسَرْ بَوْتَا، عَكَ ڨُوثٜىٰ كَايَنْمُ، عَكَسَامُ ثِكِنْ كُنْيَا كَمَرْ يَدَّ مُكٜىٰ عَيَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.