Galatians 1:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْ كُمَجٜىٰ عُرُوشَلِيمَ وُرِنْ وَطَنْدَ سُكَ رِغَانِ ذَمَ مَنْذَنِّےبَ؞ أَبِنْدَ نَيِ شِينٜىٰ، نَنْ دَنَنْ نَجٜىٰ ڧَسَرْ أَرَبِيَ، سَعَنً نَكُواْمُواْ دِمَشْڧُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.