Galatians 4:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ مِصَالِنٜىٰ، مَاتَنَّنْ بِيُ سُنْ ݣُوتَنْتَا يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ بِيُ؞ هَجٜىٰرَتُ عِتَثٜىٰ مَيْ حَيْڢُوَرْ بَايِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina'i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan.