Genesis 1:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ اللَّهْ يَثٜىٰ، «بَرِ ڧَسَا تَڢِتَرْدَ ڟِرٜىٰ ڟِرٜىٰ مَاسُ بَادَ إِرِ، دَ كُواْوَنٜىٰ عِتَتُوَ عَڧَسَا مَاسُ بَادَ یَیَ مَاسُ إِرِ، كُواْوَنٜىٰ كُوَ يَبَادَ یَیَ بِسَغَ إِرِنْسَ؞» حَكَ كُوَ يَكَسَنْثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.