Genesis 1:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ اللَّهْ يَثٜىٰ، «بَرِ حَصْكُواْكِ سُكَسَنْثٜىٰ أَسَرَرِنْ سَمَ، سُرَبَ ڟَكَانِنْ يِنِ دَ دَرٜىٰ، سُكُمَ ذَمَ عَلَمُ نَنُونَ لُواْكَتَيْ دَ ݣُونَكِے دَ شٜىٰكَرُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.