Genesis 1:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ اللَّهْ يَا حَلِثِّ مَنْيَنْ دَبُّواْبِنْ ضُوَ، دَ كُواْوَنٜىٰ أَبُ مَيْرَيْ دَيَكٜىٰ مُواْڟِ عَثِكِنْ ضُوَ بِسَغَ إِرِنْسَ، دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ ڟُنْڟُ بِسَغَ إِرِنْسَ؞ يَاغَ يَنَدَݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.