Genesis 10:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ سُونٜىٰ ظُرِيُواْيِنْ یَیَنْ نُوحُ، بِسَغَ لِسَّڢِنْ أَصَلِنْسُ، بِسَغَ ڧَبِيلُنْسُ؞ دَغَ وَطَنَّنْ نٜىٰ أَلْعُمَّيْ سُكَ يَطُ كُواْعِنَ أَ ڢُسْكَرْ دُونِيَا بَايَنْ بَبَّرْ أَمْبَلِيَرْ ضُوً؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al'ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.