Genesis 14:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ دَدَّرٜىٰ سَيْ يَرَرَّبَ مَاسُيِمَسَ يَاڧِ؞ إِبْرَمْ دَ مَاسُيِمَسَ حِدِمَ سُكَيِ تَبِنْسُ حَرْ هُواْبَ، تَأَرٜىٰوَثِنْ دِمَشْڧُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu.