Genesis 14:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki).
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنْ دَ إِبْرَمْ يَدَاوُاْ دَغَ نَصَرَرْ دَ يَيِ عَكَنْ سَرْكِے كٜىٰدُوارْلَيُواْمٜىٰرْ دَ سَوْرَنْ سَرَاكُنَنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ، سَيْ سَرْكِنْ سُواْدُوامْ يَڢِتَ دُواْمِنْ يَتَرْيٜىٰشِ أَ ݣُورِنْ شَوٜىٰ، وَتُواْ ݣُورِنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa'ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato Kwarin Sarki.