Genesis 15:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِبْرَمْ يَا كَٰوُاْ دَبُّواْبِنَّنْ أَغَبَنْ اللَّهْ ، يَا ڟَٰغَ كُواْوَنّٜىٰنْسُ أَڟَكِيَ، يَا جٜىٰرَ رَبِے طَيَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ دَامَ، رَبِے طَيَ كُمَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ هَغُ؞ عَمَّا بَيْ ڟَٰغَ ڟُنْڟَيٜىٰنْ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.