Genesis 16:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَلاَىِٕكَنْ يَثٜىٰمَتَ «هَجٜىٰرَتُ، بَيْوَرْ سَارَيَ دَغَ إِنَا كِكَ ڢِتُواْ، كُمَ إِنَا ذَاكِ؟» تَا أَمْسَ تَثٜىٰ «إِنَ غُدُ نٜىٰ دَغَ عُوَرْغِجِيَتَ سَارَيَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?” Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”