Genesis 17:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ نَنْ حَرْ إِيَاكَرْ ڟَارَرَّكِنْكُ، كُواْوَنٜىٰ نَمِجِنْ دَ عَكَ حَيْڢَ عَثِكِنْكُ، دُواْلٜىٰ عَيِمَسَ كَاثِيَ أَ رَانَ تَتَݣُوسْ، كُواْ أَنْحَيْڢٜىٰشِ أَغِدَا نٜىٰ، كُواْ أَنْسَيٜىٰشِ دَ كُطِ دَغَ حَنُّنْ وَنِ بَڧُواْ وَنْدَ بَ نَظُرِيَرْكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.