Genesis 17:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاعَ ڧَارَ كِرَنْ سُونَنْكَ إِبْرَمْ بَ، عَمَّا ذَاعَ كِرَاكَ إِبْرَٰهِيمْ؞ غَمَا نَا سَاكَ كَذَمَ بَابَنْ دُبُنْ دُبَّنْ ڧَبِيلُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.