Genesis 18:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِبْرَٰهِيمْ يَاثٜىٰ «كَدَ دَيْ عُبَنْ‌غِجِ يَيِ ڢُشِے! ذَنْ سَاكٜىٰيِنْ مَغَنَ سَوْ طَيَنَّنْ كَطَيْ؞ تُواْ دَاعَثٜىٰ ذَاعَ سَامِ غُواْمَ أَوُرِنْ ڢَا؟» سَيْ يَأَمْسَ «سَبُواْدَ غُواْمَ طِنْ، بَذَنْ هَلَّكَ وُرِنْبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.”