Genesis 18:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا طَوْكِ كِنْدِرْمُواْ دَ مَدَرَ دَ طَنْ بِجِمِنْ دَ عَكَ شِرْيَ، يَأَجِيٜىٰ أَغَبَنْسُ؞ سَعَنً يَا جَا غٜىٰڢٜىٰ يَنَ جِضَانْسُ يَايِنْ دَسُكٜىٰثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa'ad da suke ci.