Genesis 19:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَايِنْ دَ سَاڢِيَ تَايِ كُسَ، سَيْ مَلاَىِٕكُنْ سُكَ مَڟَا وَ لُوطُ سُنَ ثٜىٰوَ «تَاشِ كَطَوْكِ مَاتَرْكَ دَ یَیَنْكَ بِيُ مَاتَا وَطَنْدَ سُكٜىٰ أَنَنْ كُڢِتَ، دُواْمِنْ كَدَ حُكُنْثِنْ دَ ذَاعَيِ وَبِرْنِنْ يَهَلَكَاكُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da safiya ta gabato, mala'ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da 'ya'yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.”