Genesis 19:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَاثٜىٰ «يَا كُو إِيَايٜىٰنْغِجِنَ، إِنَ ضُواْڧُوانْكُ كُرَڟٜىٰ ذُوَا غِدَنْ بَاوَنْكُ؞ كُذُواْ كُوَنْكٜىٰ ڧَڢَاڢُنْكُ، كُݣُونَ، دَ سَسَّڢٜىٰ كُمَ سَيْ كُكَامَ حَنْيَرْكُ؞» سُكَ أَمْسَ «أَعَ، أَ ڢِيلِ نَثِكِنْ غَرِ ذَامُ ݣُونَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.” Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.”