Genesis 19:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُوطُ دَ یَیَنْسَ بِيُ مَاتَا كُوَ سُكَ بَرْ ذُواْوَرْ سُكَ ذَوْنَ ثِكِنْ تُدَّيْ، غَمَا يَنَ ڟُواْرُوانْ ذَمَ أَ ذُواْوَرْ؞ شِ دَ یَیَنْسَ بِيُ مَاتَا سُكَيِ ذَمَ عَثِكِنْ كُواْغُوانْ دُوڟٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata.