Genesis 19:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سُكَثٜىٰ «كَيْ، بَامُ وُرِے!» سُكَ كُمَ ثٜىٰ وَجُونَ «وَنَّنْ مُتُمْ بَڧُواْ نٜىٰ، عَمَّا يَنْذُ يَنَ سُواْ يَذَمَ مَنَ أَلْڧَلِ! يَنْذُنَّنْ ذَامُيِ دَكَيْ ڢِيٜىٰ دَسُو!» سَيْ سُكَڧَارَ مَڟَا وَ لُوطُ سُواْسَيْ سُنَجَنْ كُسَ دُواْمِنْ سُڢَسَ ڧُواْڢَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar.