Genesis 2:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتُمِنْ يَثٜىٰ، «يَوَّ! عَڧَرْشٜىٰ غَا كَمَنِّنَ، ڧَشِنٜىٰ دَغَ ڧَشِنَ، نَامَ نٜىٰ دَغَ نَامَنَ! ذَاعَكِرَتَ مَثٜىٰ غَمَا دَغَ مُتُمْ نٜىٰ عَكَ ثِرُواْتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.”