Genesis 2:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ يَا سَا كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ إِتَاثٜىٰ مَيْ ݣَنْ غَنِ كُمَ مَيْ بَادَ أَمْڢَانِ دُواْمِنْ عَبِنْثِ يَڟِرُواْ دَغَ ڧَسَا، تَرٜىٰدَ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ رَيْ أَڟَكِيَرْ غُواْنَرْدَ كُمَ إِتَاثٜىٰ مَيْ كَٰوُاْ سَنِنْ نَغَرْتَادَمُغُنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12