Genesis 21:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ تَتَڢِے، تَذَوْنَ طَنْ نِيسَ دَ يَرُوانْ، مِصَالِنْ نِيسَنْ هَرْبِنْ كِبِيَرْ بَكَ، غَمَا تَاثٜىٰ أَ رَنْتَ بَاتَسُواْ تَغَ مُتُوَرْ يَرُوانْ؞ دَ تَذَوْنَ نٜىٰسَ دَ يَرُوانْ، سَيْ تَڢَشٜىٰ دَ كُوكَا تَنَ هَوَيٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.