Genesis 21:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ يَنْذُ، كَرَنْڟٜىٰ مِنِ دَ سُونَنْ اللَّهْ ثٜىٰوَ بَذَاكَ ثُوثٜىٰنِ، كُواْ یَیَنَ، كُواْ ذُرِيَتَابَ؞ كَيِمَنَ أَلْحٜىٰرِ دَنِے دَ ڧَسَاتَ عِنْدَ كَكٜىٰ ذَمَنْ بَڧُنْثِ، كَمَرْ يَدَّ نَ نُونَ مَكَ أَلْحٜىٰرِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa ba za ka ci amanata, ko ta 'ya'yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”