Genesis 22:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِبْرَٰهِيمْ يَا طَغَ عِدَنُونْسَ يَا دُوبَ كٜىٰوَيٜىٰ دَشِ، سَيْ يَغَ ضَغُواْ دَ ڧَهُواْنِنْسَ عَكَڢٜىٰ ثِكِنْ طَنْ إِتَاثٜىٰنْ ڧَيَ؞ سَيْ إِبْرَٰهِيمْ يَتَڢِے يَكَامَ ضَغُوانْ يَمِيڧَشِ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا مَيْمَكُوانْ طَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa.