Genesis 22:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ دَ سَسَّڢٜىٰ إِبْرَٰهِيمْ يَا تَاشِ يَشِرْيَ جَاكِنْسَ، يَطَوْكِ مَاسُيِمَسَ حِدِمَ غُدَا بِيُ، تَرٜىٰدَ طَنْسَ إِسْحَٰڧَ؞ يَا ڢَسْكَرٜىٰ إِتَاثٜىٰنْ يِنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، سَيْ سُكَ كَامَ حَنْيَ ذُوَا وُرِنْ دَ اللَّهْ يَڢَطَا مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa.