Genesis 24:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِنْ دَ يَكَيْ بِرْنِنْ، سَيْ يَسَا رَاڧُمَنْسَ سُكَ دُرْڧُسَ عَبَاكِنْ رِجِيَ عَبَايَنْ غَرِ؞ وَنَّنْ كُوَ يَا كَسَنْثٜىٰ دَ يَمَّ دَيْدَيْ لُواْكَثِنْ دَ مَاتَا سُكَنْ ڢِتَ طٜىٰبُواْ ضُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.