Genesis 24:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ نَثٜىٰوَ طَيَ دَغَ ثِكِنْ یَنْ مَاتَنَّنْ، ‹إِنَ ضُواْڧُوانْكِ كِسَوْكَرْ دَ تُلُنْ ضُوَنْكِ كِبَانِ ضُوَ إِنْشَا؞› عِدَنْ كُمَ تَا أَمْسَ تَثٜىٰ، ‹ذَاكَ عِيَشَا، ذَنْ كُمَبَا رَاڧُمَنْكَ ضُوَ سُشَا،› تُواْ، بَرِ تَذَمَ وَدَّ كَذَاٻَا وَبَاوَنْكَ إِسْحَٰڧَ؞ تَهَكَنٜىٰ ذَنْسَنِ ثٜىٰوَ كَنُونَ وَمَيْغِدَانَ إِبْرَٰهِيمْ ڧَوْنَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”