Genesis 24:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتُمِنْ يَا شِغَ غِدَنْ؞ لَبَنْ كُوَ يَا سَوْكَرْدَ كَايَنْ رَاڧُمَنْ، يَا بَا مُتُمِنْ عَبِنْثِ دَ ثِيَوَ دُواْمِنْ رَاڧُمَنْ؞ يَا كُمَ كَٰوُاْ وَ مَيْ حِدِمَرْ إِبْرَٰهِيمْ دَ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ ضُوَ دُواْمِنْ سُوَنْكٜىٰ ڧَڢَاڢُنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi.