Genesis 24:45 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ إِنْ ڧَارٜىٰ مَغَنَ أَ ذُوثِيَاتَ، سَيْغَا رِڢْكَتُ تَا ڢِتُواْ دَ تُلُنْتَ عَكَڢَطَرْتَ تَغَنْ‌غَرَ تَطِبِے ضُوَ؞ سَيْ نَثٜىٰ مَتَ، ‹إِنَ ضُواْڧُوانْكِ كِبَانِ ضُوَ إِنْشَا؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, ‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.’