Genesis 25:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ يَارَنْ سُكَيِ غِرْمَ، إِسُوَ يَذَمَ ڠُونِنْ ڢَرَوْتَ، مُتُمِنْ دَاجِ؞ يَعْڧُوبَ كُمَ شِضُ شِضُ نٜىٰ، مَيْ ذَمَ أَغِدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida.