Genesis 25:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa ’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا غَ یَیَ مَظَا نَسَوْرَنْ مَاتَانْدَ يَأَجِيٜىٰ، إِبْرَٰهِيمْ يَابَاسُ ݣَوْتَيْ؞ تُنْ يأَنَانً دَ رَيْ يَسَلَّمٜىٰسُ دُواْمِنْ سُرَبُ دَ إِسْحَٰڧَ سُتَڢِے ڧَسَاشٜىٰنْ غَبَسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.