Genesis 26:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِسْحَٰڧَ كُمَ يَا سَاكٜىٰ حَڧَ رِجِيُواْيِنْ دَ عَكَحَڧَ أَ زَامَانِنْ بَابَنْسَ إِبْرَٰهِيمْ، وَطَنْدَ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ تُواْشٜىٰ دَ ڧَسَا بَايَنْ مُتُوَرْ إِبْرَٰهِيمْ؞ يَا كُمَ سَاكٜىٰ بَا رِجِيُواْيِنْ سُونَيٜىٰنْ دَ دَا بَابَنْسَ يَبَاسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.