Genesis 26:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَكِيَايَ نَ غٜىٰرَرْ سُكَ شِغَ غَرْدَمَ دَ مَكِيَايَ نَ إِسْحَٰڧَ سُنَ ثٜىٰوَ ضُوً نَاسُ نٜىٰ؞ سَيْ إِسْحَٰڧَ يَكِرَا رِجِيَرْ دَ سُونَ عٜىٰسٜىٰكْ، وَتُواْ «غَرْدَمَ»؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa,“Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.