Genesis 26:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot, yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا تَاشِ دَغَ وُرِنْ يَا حَڧَ وَتَ رِجِيَ، عَمَّا بَسُيِ غَرْدَمَ عَكَنْتَبَ؞ سَيْ يَكِرَا رِجِيَرْ دَ سُونَ رٜىٰهُواْبُواتْ، وَتُواْ «إِسَشّٜىٰنْ وُرِے»، يَنَ ثٜىٰوَ «يَنْذُ يَهْوٜىٰهْ يَابَامُ إِسَشّٜىٰنْ وُرِے، ذَامُ يَلْوَتَ عَڧَسَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”