Genesis 27:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.” Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَعَدَّ إِسْحَٰڧَ يَڟُوڢَ، عِدَنُونْسَ كُمَ بَاسَ عِيَ غَنِ سَبُواْدَ ڟُوڢَرْسَ، سَيْ يَكِرَا إِسُوَ طَنْسَ نَڢَارِ يَثٜىٰ مَسَ «طَانَ!» سَيْ إِسُوَ يَثٜىٰ «غَا نِے نَنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!” Sai ya amsa, “Ga ni nan.”